rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Kenya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutanen da Ambaliyar ruwa ta hallaka a gabashin Afrika sun haura 120

media
Ko a jiya Alhamis ma sai da wata gada a Kenya ta rufta tare da hallaka akalla muatne 8 duk dai sanadiyyar Ambaliyar ruwan a yankin wanda ya yi fama da fari a baya-bayan nan. rfi

Bayan kwashe makonni ana tafka ruwan sama a Yankin Gabashin Afirka da ya dade yana fama da fari, yanzu haka rahotanni sun ce wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar da aka samu sun zarce 120, yayin da dubbai suka rasa muhallin su.


A kasar Kenya, mutane 120 suka mutu a cikin watanni biyu sakamakon ambaliyar, cikin su harda wasu mutane 8 da gada ta rifta da su daren jiya alhamis.

Wannan yasa kungiyar Red Cross ta bukaci agajin Dala miliyan 5 domin kai musu dauki.

Abbas Gullet, Sakatare Janar na kungiyar Red Cross ya ce gidaje 48,177 suka lalace, abinda ya tilastawa mutane 260,200 rasa matsuguni.