rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Najeriya ta yi watsi da dokar baiwa mazaje hutu bayan haihuwa

media
Majalisar Dokokin Najeriya

Yan Majalisun Najeriya sun yi watsi da dokar nan dake neman a baiwa iyaye maza samun damar tafiya hutu lokacin da matan su suka haihu, domin taimaka musu wajen yin jego,kamar yadda ake baiwa mata.


Dokar baiwa maza hutu kamar yadda ake baiwa mata da dan Majalisa Edward Pwajok na yankin Filato ya shigar ta gamu da adawar yan majalisun da suka bayyana cewa amincewa da doka bai cancanta ba.

Yan majalisu mata dake zauren majalisar sun bayyana damuwa a farkon mahawara, idan suka nemin goyan bayan sauran yan majalisu na yi adawa da wannan bukata.

Yan Najeriya da dama ne suka nuna farin cikin su a kai tareda bayyana cewa ba wannan ne ya dami jama'a a wannan lokaci ba.