Isa ga babban shafi
Mali

Dakarun Mali sun isa birnin Kidal

Dakarun gwamnatin kasar Mali sun samu isowa garin Kidal bisa rakiyar rudunnar wanzar da zaman lafiya ta Barkhane. Wanna dai ne karo na farko da sojojin gwamnati suka sake dawowa garin Kidal tun bayan da suka fice daga yankin a shekarar 2014.

Dakarun kasar Mali a yankin arewacin kasar
Dakarun kasar Mali a yankin arewacin kasar AFP/Getty Images
Talla

Zuwan rundunar Sojin gwamnatin ta Mali a garin na kidal na daga cikin sharuddan da aka cimma tsakanin hukumomin kasar da ‘yan tawaye, wanda kuma ake sa ran sojin gwamnati da yan tawaye za su yi aiki tare wajen sa ido kan sha’anin tsaro na yankin arewaci kasar da zimmar samar da rundunar bai-daya a karkashin dokokin kasar Mali.

‘Yan tawaye a kasar Mali dai sun dade suna kaddamar da hare-hare da suke kai wa dakarun gwamnati a shekarun baya, abinda ya yi sanadin mutuwar mutane fararen Hula da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.