Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan bindiga sun hallaka mutane 52 a Birnin Gwari

Akalla rayukan mutane 52 ne suka salwanta a wani harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a arewacin tarayyar Najeriya.

Jami'an 'Yan sandan Najeriya.
Jami'an 'Yan sandan Najeriya. Reuters
Talla

Daya daga cikin shugabanni yankin Zubair Idris Abdurauf yace an kai harin ne daren jiya Asabar a kauyukan Gwaska da Kuiga Inda aka kashe mazauna garuruwan harda kananan yara.

Shugaban yankin Zubair Idris yace maharan sun fito ne daga jihar Zamfara.

Harin ya zo ne kasa da mako guda, bayan Sifeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris ya ziyarci garin inda ya sanarda tura karin yan Sanda 200.

An dai samu gawawwakin mutanen da aka kashe ne warwatse a cikin daji da ke kasa da wani kauye da ‘yan Banga suka zo domin taimaka wa, bayan jin labarin cewar ‘yan bindigar sun yi masu kawanya.

Daga Kaduna wakilinmu Aminu Sani Sado ya aiko mana da karin bayani acikin wannan rahoto da ya aiko mana.

01:34

Yan bindiga sun hallaka mutane 52 a Birnin Gwari

Aminu Sani Sado

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.