rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun hallaka mutane 9 a Taraba

media
Jihar Taraba dai yanzu haka na daga cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar barazanar tsaro. Solacebase

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta tabbatar da wani harin 'yan bindiga  a kauyen Tutuwa cikin karamar hukumar Ussa da ke jihar Taraba da aka kai da Asubahin yau wanda aka yi yakinin ya hallaka akalla mutane 9.


Kakakin 'Yan sandan jihar David Misal ya ce an kai harin ne yau da Asubahi kuma tuni mataimakin kwamishinan 'yansanda Aliyu Tafida ya ziyarci garin da lamarin ya faru.

Shugaban karamar hukumar ta Ussa, Rimansikwe Karma, ya ce an kai harin ne da misalin karfe 5 na asuba lokacin da mutanen kauyen ke tafiya wurin ibada.

Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara a Najeriyar.