Isa ga babban shafi
Kenya

Fashewar dam ta hallaka mutane 32 a Kenya

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani dam na ruwa a yankin kudancin Kenya bayan an tafka ruwan sama mai karfi a cikin daren da ya gabata.

Kenya ta yi fama da ambaliyar ruwa a 'yan makwannin nan, lamarin da a jumulce ya kashe mutane sama da 150
Kenya ta yi fama da ambaliyar ruwa a 'yan makwannin nan, lamarin da a jumulce ya kashe mutane sama da 150 Reuters/路透社
Talla

Jami’an ‘yan sandan kasar sun shaida wa manema labarai cewa, akwai mutane da dama da ke karbar magani a asibiti sakamakon raunin da suka samu a sanadiyar ibtila’in wanda ya auku a garin Solai da ke kusa da birnin Rift Valley da ke Nakuru.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kiyasta cewa, akalla iyalai 500 ne musibar ta shafa, yayin da fashawar dam din ta yi awon gaba da gidajen jama’a, in da mutane akalla dubu 2 suka rasa matsugunnansu.

An dai samu ambaliyar ruwa da kuma zabtarewar laka a Kenya bayan shafe makwannin na tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya, lamarin da ya lakume jumullar rayuka 152 kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.