rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Sudan Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kashe mataimakin jakadan Najeriya a Sudan

media
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir a fadar gwamnatin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Jami’an tsaron kasar Sudan sun tabbatar da kisan jami’in Diflomasiyyar Najeriya da ke kasar wanda aka yiwa kisan gilla ta hanyar daba masa wuka a gidansa da ke birnin Khartoum a yau Alhamis.


Hukumomi a Sudan din sun ce kawo yanzu ba a kammala bincike don gano wadanda ke da hannu a kisan jami’in ba.

Haka zalika Ofishin jakadancin Najeriya a birnin na Khartoum bai ce uffan kan batun ba.

Duk da cewa dai Sudan din ta yi fama da karancin tsaro a baya, amma kisan jami'in Diflomasiyya har gida a birnin Khartoum sabon abu ne.