rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Muhammadu Buhari

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya isa gida Najeriya daga birnin London

media
Muhammadu Buhari dai na fuskantar kalubable a Najeriyar musamman bayan bayyana ra'ayinsa na kara tsayawa takara a 2019, matakin da wasu ke ganin ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai kara tsayawa. NAN

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa babban birnin kasar Abuja da misalin karfe 7 na yammacin yau bayan shafe kwanaki uku a birnin London wajen duba lafiyarsa.


Da farko dai an shirya cewa sai a gobe ne shugaban zai koma Najeriyar amma kuma kwatsam wata sanarwar da tsakar ranar yau ta ce jirgin shugaban ya taso daga birnin London.

Kafin yanzu dai wasu na ta rade-radin cewa shugaban ka iya wuce kwanakin da ya diba na zuwa duba lafiyar ta sa la'akari da cewa a bara sai da kwashe kusan watanni uku yana jinya a birnin London.

A makon jiya ne dai lokacin da shugaban ke dawowa daga Amurka bayan ganawa da Donald Trump ya yada zango a Birtaniyar sakamakon lalacewar da jirginsa ya yi a cewar babban mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, inda kuma daga nan ne ya gana da likitansa wanda ya bukaci ya koma don duba lafiyarsa.

Bayan dawowar shugaban a wancan makon ne kuma, ya rubuta bukatar zuwa ganin Likita inda ya tafi birnin na London a ranar talatar da ta gabata don yin kwanaki hudu, amma kuma daga bisani aka sauya zuwa kwanaki uku bayan da shugaban ya kammala duba lafiyar ta sa.

Muhammadu Buhari dai na fuskantar kalubable a Najeriyar musamman bayan bayyana ra'ayinsa na kara tsayawa takara a 2019, matakin da wasu ke ganin ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai kara tsayawa.