rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kura-kurai ne suka hadasa mutuwar sojan Amurka a Nijar

media
Sojojin Amurka dake aikin tsaro a wasu kasashen Duniya THOMAS COEX / AFP

Wani rahotan binciken da rundunar sojin Amurka ta gudanar ya bayyana cewar jerin kura kurai ne suka yi sanadiyar kisan da yan ta’adda suka yiwa sojojin kasar a Jamhuriyar Nijar.


Kazamin harin da aka kai kan sojojin Amurka a watan Oktoban bara da yayi sanadiyar halaka sojoji guda 4 ya jefa shakku kan rawar da sojojin ke takawa a yankin wajen yaki da ta’addanci, yayin da ya haifar da zazzafar mahawara kan dalilin su na zuwa Nijar.

Rahotan binciken da sojojin suka yi, yace kura kurai daga jami’ai da kuma rashin horo da kuma fahimtar yanayin yankin da suka samu kan su ya taimaka wajen samun hadarin.

Rahotan ya ce sojojin basu yi atisaye tare ba ko kuma tintibar manyan su, lokacin da suka tafi aiki a kusa da kauyen Tiloa dake Nijar, abinda ya kaiga afka musu.

Wani babban hafsan sojin Amurka bara ya bayyana cewar an kai hari kan sojojin ne a kauyen Tongo Tongo lokacin da suka tsaya bayan dawowa daga inda suka yi aiki, abinda ya baiwa yan bindigan kimanin 50 damar kai musu hari.

Rahotan ya ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa sojojin suka dauki kusan awa guda kafin neman taimako bayan kai musu harin.

Yanzu haka Amurka na da sojoji 800 da jiragen sama masu sarrafa kan su a Yameh dake Nijar, yayin da take gina sabon sansani a Agadez da zai ci Dala miliyan 100.