rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Congo Brazaville

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za a garkame tsohon hafsan soji tsawon shekaru 20 gidan yari

media
Tsohon babban hafsan sojin kasar Congo Jean-Marie Michel Mokoko a lokacin da ake yanke masa hukunci a birnin Brazzaville. REUTERS/Roch Bouka

Wata kotun kasar Congo ta yanke hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 20, akan tsohon babban hafsan sojin kasar, kuma dan takarar shugabancin kasar Jean-Marie Michel Mokoko.


Kotun ta samu Mokoko ne da laifin barazana ga tsaron kasa da kuma mallakar muggan makamai ba bisa ka’ida ba.

Makoko ya taba tsayawa takarar kujerar shugabancin kasar Congo a watan Mayu na shekarar 2016, inda ya sha kaye a hannun shugaba mai ci Denis Sassou Nguesso.

A watan Yuli na shekarar ta 2016, aka kame Makoko da wasu makusantansa, bisa zarginsu da yunkurin yiwa shugaba Sassou Nguesso juyin mulki a shekarar 2005.

Makoko wanda yake da ragowar kwanaki uku domin daukaka kara, yaki baiwa kotu bayanan da ta bukata a lokacin da ake gudanar da shari’ar tasa da aka fara ta a ranar Litinin da ta gabata, a cewarsa yana rike da lambar girmamawa ta rundunar sojin kasar, wadda ta bashi kariya daga kowane irin hukunci.