rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sama da Mutane miliyan 7 na bukatar agaji a Sudan

media
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kin bai wa Sudan taimako zai jefa rayuwar mutane akalla miliyan 3 da rabi cikin hadari. AP Photo/Sam Mednick

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kara yawan agajin da kasashen duniya ke bai wa Sudan saboda yadda dubban al’ummar kasar ke bukatar taimako sakamakon matsalar tattalin arziki da kuma tabarbarewar al’amura.


Mark Lowcock, shugaban hukumar agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kungiyoyin agaji da su bada taimakon kusan Dala biliyan daya da rabi domin taimakawa mutane sama da miliyan 7 da ke bukatar agajin.

Tashe tahsen hankulan da ake samu a kasar sun raba miliyoyin mutane da matsugunan su.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kin bai wa Sudan taimako zai jefa rayuwar mutane akalla miliyan 3 da rabi cikin hadari.