Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta yi umarnin tsare tsohon gwamnan Plateau

Wata Kotu a garin Jos da ke Najeriya ta bada umurnin tsare tsohon Gwamnan Jihar Plateau kuma Sanata mai wakiltar Plateau ta Arewa, Jonah Jang, saboda zargin da Hukumar EFCC ke masa na karkata sama da naira biliyan 6 kudin al’ummar Jihar.

Kotun dai ta ce bayar da belin Jonah Jang ka iya zama barazana ga shaidun da EFCC ke da ita kan shri'ar cin hancin da ake masa.
Kotun dai ta ce bayar da belin Jonah Jang ka iya zama barazana ga shaidun da EFCC ke da ita kan shri'ar cin hancin da ake masa. NAN
Talla

EFCC ta ce tsohon Gwamna Jong ya hada baki da wani Sakataren kudi a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Yusuf Pam wajen karkata makudan kudaden lokacin da ya ke rike da mukamin Gwamna.

Jonah Jang yaki amincewa da zargin, yayin da lauyansa Robert Clarks ya bukaci kotu ta bada belinsa amma sai lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya ce ba da shi beli na tattare da hadari saboda ya na iya razana shaidun da suke da shi, a matsayin sa na tsohon Gwamnan soji da kuma farar hula.

Daga bisani alkalin kotun Daniel Longji ya ki bada beli, inda ya umarci a tsare tsohon Gwamnan a gidan yarin Jos har zuwa ranar 24 ga watan Mayu da za’a cigaba da sauraron shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.