rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Bindiga sun toshe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari

media
Sojin Najeriya

A Jihar Kadunan Najeriya akalla mutane kusan 100 yan bindiga suka yi garkuwa da su akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, bayan sun tare hanyar motar dauke da muggan makamai.


Kamfanin Dillancin Labaran Reuters ya jiyo daga bakin Suraju Usman, wani direban kungiyar direbobin motocin sufuri na kasa, da ya tsallake rijiya da baya, na cewa lamarin ya faru ne kwanaki biyu da suka gabata.

Sai dai kwamishinan yan Sandan Jihar Austin Iwar yace basu da masaniya dangane da wannan labari.

Mazauna yankunan na cigaba da yi kira zuwa hukumomin Najeria na taimaka domin kawo karshen wannan lamari da aka jima ana fama da shi.