rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ebola ta watsu zuwa birane a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

media
La dernière épidémie en RDC remonte à 2017. Ici sur la photo des mesures de quarantaine prises à Muma, en juin 2017. la maladie était réapparue début mai dans une zone boisée du nord-est du pays et avait provoqué la mort de 4 des 8 personnes infectées. JOHN WESSELS / AFP

Kungiyar lafiya ta Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewar an samu rahotannin da ake nuni akan cewar Cutar Ebola ta watsu zuwa wasu birane da ke cikin kasar, abinda ke kara fargabar da ake na yiyuwar cutar ta kara kamari a cikin kasar.


A baya bayan nan ne aka samu labarin wani mutum da ya kamu da Cutar ta Ebola a Wangata dai daga cikin cibiyoyin kiyon lafiya uku da ke a Mbandaka wani birni mai kumshe da akalla mutane miliyan 1 da dubu 200 a Lardin Equateur da ke a Arewa maso yammacin jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Dama dai hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashin farko na maganin riga-kafin cutar ebola 4,000 ya isa Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo domin amfani da shi wajen rigakafi a yankin Bikoro da cutar ta hallaka mutane 20.

Kakakin hukumar Tarik Jasarevic ya ce za a yi amfani da riga-kafin ne a kan mutanen da aka tabbatar sun yi mu’amala da wadanda suka kamu da cutar.

Hukumar ta shirya fara bada maganin ranar litinin mai zuwa, amma ma’aikatar lafiyar Congo ta ce ana iya fara aikin a karshen mako mai zuwa.