rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasar Filifinu ta dage sanke ga masu ci rani a Kuwaiti

media

Hukumomi a kasar Filifinu sun dage sanken da suka saka wa ‘yan gudun hijirar da ke barin kasar ta Filifinu zuwa kasaar Kuwaiti domin neman ayyukan yi.


Wannan matakin na saka sanke ga al’ummar kasar da ka je ci rani a Kuwaiti daga kasar ta Filifinu dai ya samo asali ne daga matsalar Diplomasiyyar da aka sama a tsakanin kasashen biyu a baya.

Wannan labarin dai ya fito fili ne bayan da kasashen biyu suka kulla wata yarjejeniyar tsaftace hanyar neman ayyukan yi da batun biyan kudi masu tsoka da ‘yan kasar ta Filifinu ke nema a kasar Kuwaiti.

Alkalumman kididdiga sun nuna cewar akalla yan kasar Filifinu 262,000 ne aka tabbatar suna aiki a kasar Kuwaiti, kashi 60 daga cikinsu kuma na aiki ne a cikin gidaje.

Wannan adadin dai na daga cikin miliyoyin yan kasar da hukumomin kasar suka aika domin yin ayyuka a kasashen waje domin neman albashin da basa samu a kasarsu.

Kuma kashi 10 na tattalin arzikin kasar duka na fitowa ne daga kudaden da ma’aikatan ke aikewa kasar daga kasashen waje ne.

 

Karuwar sarrafa ababen bukata a Amurka

 

A cikin watan Afrilun da ya gabata an samu karuwar yadda ake sarrafa ababen bukata a kasar Amurka sakamakon yanayin sanyi da aka yi fama da shi a masana’antun kasar Amurka.

Masana harkokin tattalin arziki sun ce, an samu karuwar kayan da masana’antu ke sarrafawa da akalla digo 7 ne idan aka kwatanta da yadda yake a digo 3 a watan Maris da ya gabata, kuma wannan ya nuna yadda aka samu habakar al’amurran ne da akalla kashi 3.5 sama da wanda aka samu a watan Afrilun shekarar 2017.

 

Hukumar EFCC ta gano kudin sata naira miliyan 500

 

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu, ya ce hukumarsa ta samu nasarar kwato kudaden sata da yawansu ya haura Naira Biliyan 500.

Magu ya ce an samu wannan nasara ce bayan karbar jagorancin hukumar da ya yi zuwa yanzu.

Magu wanda ya bayyana haka yayin bude sabuwar sakatariyar hukumar EFCC, ya kara da cewa, an samu nasarar yanke hukunci akan wadanda aka samu da laifin sata ko cin hanci da Rashawa akalla 486 daga watan Nuwamban 2015 zuwa yanzu.

 

Babban Bankin kasar Tanzaniya ya amince da hadewar bankuna biyu

 

Babban Bankin kasar Tanzaniya ya ce ya amince da shirin hadewar wasu kananan Bankuna biyu na kasar da ake kira Twiga Bancorp da TPB Bank dukansu da ke kokarin hadewa domin maido da darrajar kudaden kasar da kuma rage yawan masu neman rance a cikin kasar.

Wannan matakin da Bankunan biyu suka dauka tare da amincewar babban Bankin kasar na kuma da manufar rage yawan basussuka marasa alfanu da ake yawan dauka a kasar abinda ya tagayyara ribar da Bankunan ke samu ta hanyar ara wa kamfunna da hukumomi masu zaman kansu kudi da ya shafi tafiyar tattalin arzikin kasar a shekarar 2015.

Mataimakin Manajan babban Bankin Bernard Kibesse ya ce ko baya ga wannan hadewar ta Bankunan biyu, haka ma a nan gaba za’a ga yadda wasu Bankunan kasar za su kara hadewa duka domin magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

A cikin watan Okotoban Bara dai daukacin harkokin cinikayyar da Bankin Twiga Bancorp ya yi a karkashin jagorancin babban Bankin ne.