rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muslmin Najeriya sun fara Azumin Ramadana

media

Al’ummar Musulmi a tarayyar Najeriya sun fara azumin watan Ramadan kamar yadda takwarorin sun a duniya suka fara tare da kasashen Saudi Arabiya da hadaddiyar Daular Larabawa.


Wannan ya biyo ganin jinjirin watan da aka yi jiya kamar yadda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar lll ya sanar da yammacin Laraba.

Mai Alfarma sarkin Musulmin ya bayyana cewar an sami labarin ganin sabon watan ramadana daga shugabanni da kungiyoyin addinin musulunci daban daban daga manyan garuruwan kasar Hausa kamar Sokoto da Maiduguri da Damaturu da Dutsi da Minna da Fatakwal da Zamfara da Bauchi da Gombe da dai sauran garuruwa masu yawa.

A cewar mai Alfarma Sarkin Musulmi kwamitocin ganin wata na wadannan garuruwa sun tantance da ganin watan, ita kuma fadar Mai Alfarma sarkin Musulmi ta tabbatar da hakan, don haka Alhamis 17 ga watan Mayu 2018 ta kasance 1 ga watan Ramadana na 1439 bayan hijira.