rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yake-yake na tilasta wa mutane barin matsugunnansu

media
Wani yaro kenan a tsugunne yana kallon sansanin 'yan gudun hijira na Rohingya ©REUTERS/Andrew RC Marshall

Wata Cibiyar mai sa ido kan mutanen da suka rasa muhallansu ta duniya ta ce, a kowacce rana yake-yake na tilasta wa mutane dubu 15 ficewa daga gidajensu a kasashen da ke Kudu da Sahara muasamman a shekarar da ta gabata, adadin da ya rubanya wanda aka samu a shekarar 2016.


Cibiyar ta IDMC ta bukaci karin bada tallafi ga wadanda suka rasa muhallansu a cikin kasashensu na asali, kuma a cewarta, yankin Kudu da Sahara na dauke da kusan rabin jimillar mutane miliyan 11. 8 da suka rasa gidajensu a kasashen duniya daban-daban sakamakon tashe-tashen hankula a bara.

Daraktar cibiyar mai Ofishi a birnin Geneva, Alexandra Bilak ta ce, wannan matsalar ce ke haifar da tsallake-tsalleken iyakokin kasashe, abin da ta ce, ka iya tsananta rikici, lura da yadda kasashen da ke karbar sabbin baki ke fafutukar samar musu da matsugunnai.

Bilak ta ce, ga alama kasashen duniya sun karkata hankulansu kacokan kan matsalar ‘yan gudun hijira kadai, amma sun yi watsi da sha’anin wadanda suka rasa gidajensu a cikin kasashensu na asali ba tare da ba su isasshen tallafi ba.

Darektar ta bayyana fatan wannan rahoton da suka fitar zai zaburar da kasashen duniya wajen daukan matakin da ya dace na dakile ko kuma rage matsalar rasa muhallai.

Jamhuriyar Dimkoradiyar Congo dai ita ce ta fi fama da matsalar rasa muhalli, in da a bara aka samu kusan miliyan 2.2 a kasar kadai.

Sai Sudan ta Kudu da Habasha da Afrika ta Tsakiya da aka samu jumullar mutane miliyan 2.1