rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Najeriya Ta'addanci Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rahoto kan garkuwar da 'yan bindiga suka yi da jama'a a birnin Gwari

media
Hanyar ta Kaduna na neman zama babbar barazana musamman ga matafiya a Najeriyar wadanda ke ratsawa don kai wa ga wani yanki na kasar. Solacebase

Duk da Matakin da Gwamnatin Tarayyar Nigeriya ta bi na kara yawan jami’an tsaro a yankin Birnin Gwari, har yanzu ba ta canza zani ba, domin yan bindigan na ci gaba da kai hare hare tare kuma da yin garkuwa da mutane a hanyar kaduna zuwa Birnin Gwari. Ko a ranar Talatan nan, sai da suka  kai hari a wasu kauyuka guda hudu,wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.Wannan lamari ya jefa al’ummar yankin da kuma direbobi da ke zirga zirga a hanyar cikin wani mawuyacin hali.Wakilin mu daga kaduna Aminu Sani Sado na dauke da rahoto akai.


Rahoto kan garkuwar da 'yan bindiga suka yi da jama'a a birnin Gwari 18/05/2018 - Daga Aminu Ahmed Manu Saurare