rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Nijar Benin Togo Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rundunar hadin gwiwa ta kama mutane 202 bisa zargin alaka da ta'ddanci

media
Sojojin kasashen Ecowas cikin aikin tsaro RFI / Guillaume Thibault

Hadin gwiwar rudunonin tsaron kasashen Ghana, da Togo da Benin da kuma Burkina Faso sun yi nasarar kamo mutane 202 a kan iyakokin kasashen su daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan watan da muke cikin sa., wadanda ake zargi da aikata laifuffuka daban daban.


Kanal Blaise Ouedrago shugaban rudunonin kasashen hudu dake aiki tare yace sun kama mutane 52 a Burkina Faso, 42 a Jamhuriyar Benin, 95 a Togo sai kuma 13 a Ghana.

Jami’in yace wasu daga cikin mutanen da aka kama na dauke da kayayyakin hada bama-bamai, wasu da bindigogi, banda haka sun yi nasara kama Babura 623 da ake amfani da su a kan iyakokin kasashen ba bisa ka’ida ba.

Hukumomin kasashen sun tabbatar da ci gaba da gudanar da irin wadanan ayyukan hadin gwiwa domin kawo karshen ayyukan ta’adanci daga mutane bata gari.