Isa ga babban shafi
Najeriya

Magu ya zama jagoran hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Afrika

An zabi mukkadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu, a matsayin sabon shugaban hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na ilahirin kasashen kungiyar Commonwealth da ke nahiyar Afrika.

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu.
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu. Twitter/@officialEFCC
Talla

Shugabannin hukumomin sun cimma matsayar nada Magu a matsayin shugabansu, bayan kammala taron da suka yi tsawon kwanaki 5, a birnin Abuja Najeriya.

Taron hukumomin yaki da cin hanci da rashawan, mayar da hankali kan yadda kasashen na Afrika manbobin commonwealth, zasu karfafa alakar aiki tare wajen dakile yunkurin masu satar kudaden al’umma na fitar da su don boyewa a ketare, tare da kuma kwato wadanda aka riga aka karkatar a ciki da wajen nahiyar.

Taron ya kuma bukaci gwamnatocin nahiyar Afrika su kafa, tare da karfafa dokokin fallasa kudaden sata, da kuma kare wadanda ke fallasar daga dukkanin wata barazana, don cimma burin magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yiwa gwamnatotin nahiyar katutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.