Isa ga babban shafi
Najeriya

Cibiyar Lafiya a Yola ta yi nasarar raba tagwayen da aka haifa a hade

Cibiyar kula da lafiyar Gwamnatin Najeriya da ke birnin Yolan Jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin kasar ta yi nasarar aikin raba wasu tagwaye da aka haife su manne da juna a kirji. Wannan dai babbar nasara ce ga fannin lafiyar Najeriyar, la'akari da cewa a baya sai an fitar da irin wadannan jarirai kasashen ketare kafin yi musu Tiyata. 

Fatima da Maryam kenan bayan likitoci sun yi nasarar raba su a cibiyar kula da lafiya da ke garin Yolan jihar Adamawa.
Fatima da Maryam kenan bayan likitoci sun yi nasarar raba su a cibiyar kula da lafiya da ke garin Yolan jihar Adamawa. rfihausa
Talla

Yaran mata wadanda aka bayyana sunansu Fatima da Maryam sun shafe akalla watanni 5 kirjin su manne da juna kafin daga bisani likitoci a cibiyar lafiyar ta Yola su yi musu tiyata don raba su a makon jiya.

Muhammad Rawad shi ne mahaifin yaran ya ce tun farko sun yi jewar zuwa Asibiti a Maiduguri amma daga bisani aka mayar da su Cibiyar lafiyar ta Yola sakamakon a nan ne ake da likitan da ya taba gudanar da irin aikin kuma aka yi nasara.

Itama mahaifiyar tagwayen Yelwa Adam Ibrahim wadda ta ce dama tun farko tiyata aka yi mata don fitar da yaran a Asibitin da kr birnin Maiduguri, ta ce yanzu haka yaran na samun cikakkiyar lafiya tun bayan aikin, sai dai ta ce har ya zuwa yanzu yaran basa karbar Nono.

A baya dai Najeriyar kan tura irin wadannan tagwaye ne zuwa Turai don yi musu tiyata a raba su, ko da dai likitan da ya jagoranci aikin kuma shugaban cibiyar Farfesa Awwal Abubakar ya ce hantar jariran ce a hade da kuma wasu kasusuwa na kasan hakarkarin su.

Farfesa Awwal tabbas tiyatar ta yi nasara wadda aka shafe akalla sa'o'i 4 ana yi, abin da suke jira yanzu bai wuce murmurewar yaran ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.