rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fararen hula 12 sun mutu a harin ta'addanci a Mali

media
Wasu train jami'an tsaron Mali kenan da ke aikin Sintiri a yankin da ke fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi. Philippe Desmazes/AFP

Akalla fararen hula 12 sun rasa rayukansu a arewacin kasar Mali, a harin da wasu mayaka suka kai kan wata kasuwa da ke garin Boulekessi a gaf da iyakar kasar ta Mali da Burkina Faso.


Wata majiyar rundunar sojin ta Mali ta ce ana fuskantar wahalar sha'anin sadarwa da garin na Boulekessi, abinda yasa har yanzu ba’a kai ga tantance ko an samu karuwar wadanda suka hallaka ba, da kuma wadanda suka jikkata.

Mali dai na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu da'awar jihadi, wanda a lokuta da dama kan haddasa asarar dubban rayuka.

Haka zalika kasar na cikin kasashen Sahel da aka kafa runduna ta musamman don yakar ayyukan ta'addancin da suka yi kamari a cikinsu.