rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Majalisar Dinkin Duniya Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An ceto baki kusan 400 a saharar Nijar

media
An ceto kusan mutane 400 da ke cikin mawuyacin hali a tsakiyar Sahara a Nijar bayan sun yi yunkurin tsallakawa Turai ©Abdullah DOMA/AFP

Hukumar Kula da kaurar jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla baki kusan 400 'yan Afirka aka ceto a tsakiyar sahara bayan sun fada cikin halin kuncin na rashin abinci da ruwan sha a makon jiya.


Sanarwar hukumar ta ce, mutane 386 daga kasashe 3 sun shiga tsaka mai wuya ne tsakanin yankin Arlit da Assamaka da ke kusa da iyakar Algeria akan hanyarsu ta zuwa Turai.

Hukumar ba ta sanar da kasashen da bakin suka fito ba da kuma dalilin da ya jefa su cikin halin da suka samu kan su a ciki ba, sai dai ta ce, yanzu haka daukacin mutanen na samun mafaka a wani da ke Arlit, in da ake kula da su.

Hukumar ta ce, a cikin wannan shekara ta kai irin wannan dauki har sau 18, in da ta ceto ire-iren wadannan baki kusan 3,000.