Isa ga babban shafi
Congo Dimokuradiyya

Ganawar yan adawan Congo da asusun lamuni na IMF

Yan adawan Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun bukaci hukumar bada lamuni ta Duniya da ta sanya ka’idar sakin shugaba su Jean-Marie Michel Makoko a matsayin daya daga cikin sharadodin baiwa kasar rance.

Jean-Marie Michel Mokoko daya daga cikin masu adawa da Shugaban kasar Congo dake a tsare yanzu haka
Jean-Marie Michel Mokoko daya daga cikin masu adawa da Shugaban kasar Congo dake a tsare yanzu haka REUTERS/Roch Bouka
Talla

Lauyoyin Makoko, Jessica Finell da Etienne Arnaud sun rubutawa shugabar hukumar lamunin Christine Lagarde inda suke bukatar ta da ta amince da shawarar domin kawo karshen take hakkin Bil Adama da gwamnatin kasar keyi.

Makoko wanda tsohon Janar na sojin Congo ne, yayi takarar shugabancin kasar tare da shugaba Joseph Kabila a shekarar 2016, kafin kotu ta daure shi shekaru 20 a gidan yari wannan watan saboda zargin yunkurin kifar da gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.