rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sahel Amurka Faransa Majalisar Dinkin Duniya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta ki amincewa da bukatar karfafa rundunar G5 Sahel

media
Wasu daga cikin dakarun rundunar ta G5 Sahel. ISSOUF SANOGO / AFP

Kasar Amurka ta ki amincewa da bukatar ganin Majalisar Dinkin Duniya ta karfafa goyan bayan rundunar sojin G5 Sahel da ke yaki da Yan ta’adda a Afirka ta Yamma.Matakin dai na zuwa a dai dai lokacin da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da rundunar ke fatan ganin bayansa ke kara ta'azzara a yankin na Sahel.


Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya bukaci kwamitin Sulhu da ya amince da shirin bai wa rundunar kudi kowacce shekara, yayin da itama Faransa ta bukaci taimakawa rundunar, amma sai Amurka ta ce ba zata goyi bayan shirin ba.

Rundunar wadda ke da sojoji 5,000 daga kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar, da kuma taimakon sojojin Faransa ta samu tallafin kudin da ya kai Dala miliyan 500 domin gudanar da ayyukan ta.