Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Fashewar Gurneti ya hallaka mutane 12 a Bangui

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce akalla mutane 12 aka kashe sakamakon fashewar wani gurneti a unguwar da Mabiya addininin Musuluni ke da rinjaye a Bangui da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Yanzu haka akwai tarin jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da tsaro a kasar mai fama da tashe-tashen hankula.
Yanzu haka akwai tarin jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da tsaro a kasar mai fama da tashe-tashen hankula. AFP
Talla

Kungiyar agajin ta ce bayan fashewar gurnetin an kuma samu barkewar tashin hankali tsakanin mazauna yankin da basa ga maciji da juna.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da zaman lafiya a kasar sun sanar da kaddamar da bincike akai.

Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula yanzu haka akwai tarin jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aiki don ganin kawo karshen matsalar da ta ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.