rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu kasashen Afrika sun tafka asara daga 2012 zuwa yanzu

media
Bankin raya masana'antu a kasar Togo Danita Delimont/Gettyimages

Bankin tallafawa raya kasashen Afrika AFDB ya ce kasashen nahiyar Afrika sun yi asarar dala biliyan 72 daga shekarar 2012 zuwa yanzu, sakamakon durkushewa ko koma bayan ayyukan manyan masana’atunsu.


Shugaban bankin Dr Akinwumi Adesina, ya ce Najeriya, Afrika ta Kudu, Masar da kuma Algeria asarar ta fi shafar su a dalilin raguwar ayyuka ko durkushewar masana’atunsu, lamarin da ya haddasa karuwar rashin guraben ayyukan yi da ke ci wa al’ummomin kasashen tuwo a kwarya.

Kiran Shugaban  bankin Dr Akinwumi Adesina na zuwa ne  a dai-dai lokacin da aka kawo karsehn taron da ya hada wakilan kasashen Afrika da  wasu manyan yan kasuwa a Korea ta Kudu, wanda kuma Korea ta Kudu ta yi alkawalin bayar da tallafi zuwa Nahiyar Afrika.