rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China Burkina Faso

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Burkina Faso ta mayar da huldar jakadanci da China

media
Alpha Barry Ministan harakokin wajen kasar Burkina Faso AFP

Kasar Burkina Faso yau lahadi ta kulla huldar diflomasiya da China kwanaki biyu bayan ta katse da hulda da Taiwan.

Ministan harkokin wajen Burkina Faso Alpha Barry yau ya sanya hannu kan yarjejeniyar kulla huldar da takwaran sa na China Wang Yi a Beijing.


Kasar Burkina ce kasa ta biyu da ta katse hulda da Taiwan a cikin wata guda, matakin dake nuna cewar yanzu haka kasashe 18 ne kawai ke huldar diflomasiya da Taiwan a fadin duniya.

Ministan kasar China Wang yace kasa da yanzu haka ta rage a Afirka dake hulda da Taiwan, kuma suna kokarin janyo ta.