Isa ga babban shafi
Najeriya

Yemi Osinbajo ya gana da mambobin APC masu barazanar ficewa

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da tawagar ‘ya'yan jam’iyyar APC da ke barazanar ficewa daga Jam’iyyar saboda abinda suka kira yadda aka mayar da su saniyar ware.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. citypeopleonline
Talla

Rahotanni sun ce, Osinbajo ya gana da tawagar wadda ke karkashin shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da shugaban Majalisar wakilai Yakubu Dogara a fadar gwamnati.

Sauran wadanda suka halarci taron daga bangare masu barazanar ficewar sun hada da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed da tsaffin gwamnonin Kano da Adamawa da Gombe, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Murtala Nyako da Sanata Danjuma Goje.

Babu dai bayani kan tattaunawar da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.