Isa ga babban shafi
Libya-Faransa

Bangarorin hamayya a Libya sun amince da gudanar da zaben kasar

Bangarori masu hamayya da juna a rikicin Libya sun amince a gudanar da zaben shugabancin kasa da na ‘yan Majalisar dokoki a ranar 10 ga watan disamba mai zuwa a kasar.An dai cimma wannan jituwa ce a taron kasa da kasa da aka shirya yau talata, karkashin jagorancin shugaban Faransa Emmanuela Macron a birnin Paris.

Wannan ne dai karon farko da bangarorin siyasar ta Libya suka amince da zama a teburi guda karkashin jagoranci shugaba Emmanuel Macron na Faransa da nufin daidaita kasar mai fama da rikici.
Wannan ne dai karon farko da bangarorin siyasar ta Libya suka amince da zama a teburi guda karkashin jagoranci shugaba Emmanuel Macron na Faransa da nufin daidaita kasar mai fama da rikici. Reuters
Talla

Taron ya samu halartar bangarorin siyasar da suka hada da Firaminista Fayez al-Sarraj da ke samun goyon bayan MDD, da Khalifa Haftar babban hafsan soji da ke rike da muhimman yankunan gabashin kasar, sai kuma shugabannin majalisun dokokin rikon kwaryar kasar biyu.

Taron ya amince cewa, kafin ranar 16 ga watan satumba mai zuwa ne za a kammala aikin rijistar masu zabe, daga nan kuma sai a fara karbar takardun ‘yan takara domin dora kasar a kan turbar dimokuradiyya.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ke daukar nauyin taron, ya ce wannan alama ce da ke tabbatar da cewa Libya ta dau hanyar samun zaman lafiya.

Wannan ne karo na farko a irin wannan yanayi da illahirin magabatan kasar Libya duk da bambacin ra’aoyi a tsakaninsu, amma suka zauna kan teburi daya domin yin aiki tare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.