rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Gernot Rohr ya bayyana sunayen yan wasan Najeriya 23 da zasu wakilci kasar a Rasha

media
Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Reuters/Peter Cziborra

Mai horar da yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya bayyana sunayen ‘yan wasan kasar 23 da zasu fafata a gasar cin kofin duniya da za’a fara ranar 23 ga watan nan a Rasha.


Bayan karawar da kungiyar tayi da Ingila, Rohr ya sauke ‘yan wasa biyu daga cikin 25 da ya tafi da su da suka hada da Ola Aina da Mikel Agu.

Wadanda suka samu shiga sun hada da masu tsaron gida 3 da ‘yan tsaron baya 8 da ‘yan tsakiyar fili 6 da ‘yan wasan gaba 6.

Sunayen masu tsaron gidan sun hada da Ikechukwu Ezenwa da Daniel Akpeyi da Francis Uzoho. Yan wasan baya sun hada da Wiliam Ekong da Leon Balogun da Kenneth Omeruo da Bryan Idowu ad Chidozie Awaziem da Abdullahi Shehu da Elderson Echiejile da Tyronne Ebuehi.

Yan wasan tsakiya sun hada da kaftin Mikel John Obi da Ogenyi Onazi da John Ogu da Wilfred Ndidi da Oghenekaro Etebo da Joel Obi.

Sai kuma yan wasan gaba da suka hada da Odion Ighalo da Ahmed Musa da Victor Moses da Alex Iwobi da Kelechi Ihenacho da Simeon Nwankwo.

Najeriya zata kara da Croatia da Iceland da kuma Argentina a zagayen farko.