rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo WHO Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 5 sun sake kamuwa da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo

media
Wasu jami'an lafiya da ke lura da masu fama da cutar Ebola a Jamhuriyar Congo. AFP Photo/Junior D. Kannah

Ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Congo sun sanar da gano wasu karin mutane 5 da suka kamu da cutar Ebola, a yankin arewa maso yammacin kasar.


Uku daga cikin mutanen mazauna kauyen Bikoro ne, inda cutar ta fara sake bulla a makwannin baya, yayinda sauran biyun da suka kamu ke Wangata.

Sabon al’amarin yazo ne a dai dai lokacin da hadin gwiwar gwamnatin jamhuriyar Congo da hukumar lafiya ta duniya WHO ke kokarin shawo kan cutar da ta sake barkewa a makwannin baya, inda zuwa yanzu sama da mutane 50 suka sake kamuwa da ita, wasu 25 kuma suka mutu a dalilin cutar.

Ranar 8 ga watan Mayu da ya wuce, ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Congo, ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola a kauyen Bikoro da ke arewa maso yammacin kasar.