Gwamnatin Buhari ta kashe dala biliyan 9 a ayyukan raya kasa
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kashe dala biliyan 9, kwatankacin sama da naira tiriliyan 2 da rabi, wajen aiwatar da wasu ayyukan raya kasa da suka kunshi gina hanyoyi, layin dogo da kuma lantarki a cikin shekaru 2.
Wallafawa ranar:
Shugaba Buhari wanda sakataren gwamnati Boss Mustafa ya wakilta, ya bayyana haka ne a wurin taron hukumar bunkasar yawon bude idanu ta Majalisar Dinkin Duniya karo 61, sashin lura da nahiyar Afrika, wanda ya gudana a Abuja.
Shugaba Buhari ya ce shirin bangare ne na yunkurin gwamnatinsa wajen sauya dogaron tattalin arzikin Najeriya daga man fetur, ta hanyar bunkasa, fannonin Noma, hakar ma’adanai, da kuma yawon bude ido.
Taken taron da ya samu halartar wakilan kasashe 53 shi ne kididdiga kan bunkasar sashin bude idanu, a matsayin kashin bayan ci gaban tattalin arziki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu