rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bakin-haure Habasha Somalia Yemen

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bakin-haure sama da 40 'yan kasar Habasha sun hallaka

media
Jami'an ceto tare da wasu bakin-haure da suka ceto daga teku, yayin da jirginsu ya kife, a lokacin da suke kokarin zuwa kasar Yemen. AFP/IOM

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya IOM, ta ce akalla bakin-haure 46 sun rasa rayukansu wasu 16 kuma suka bace, sakamakon nutsewar da suka yi a teku ranar a Laraba.


Hukumar ta IOM, ta ce baki dayan bakin-hauren 46 ‘yan kasar Habasha ne.

Hadarin ya auku ne yayin da jirgin ruwan da ke safarar bakin-hauren akalla 100 ke kokarin ketara teku zuwa kasar Yemen, bayan barin yankin Bossasso da ke Somalia.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta duniya, ta ce a kowane wata, sama da bakin-haure 7, 000 ke kokarin yin baluguro da ke cike da matukar hadari daga nahiyar Afrika zuwa Yemen, ta hanyar ketara teku.