rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar dattijan Najeriya ta bukaci ayyana Abiola shugaban kasar

media
Zaman majalisar Dattijan Najeriya. Nigeria National Assembly

Majalisar Dattijan Najeriya ta bukaci bayyana Chief Moshood Abiola a matsayin tsohon shugaban kasa da kuma biyan sa hakkokin sa na shugaban kasa kana da bayyana sakamakon zaben 12 ga watan Yuni na shekarar 1993 wanda ake cewa shi ya lashe.


Bayan tafka mahawara kan bayyana matsayin ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokiradiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, Majalisar ta ce har yanzu ranar 29 ga watan Mayu ita ce ranar rantsar da shugaban kasa, kana babu yadda za’a dauki wani mataki irin wannan ba tare da yin doka ba.

Ko da wasu na ganin yunkurin na Majalisar Dattijan abin maraba amma masana na ganin bukatar ta su ka iya zama babbar barazana ga siyasar kasar.