rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni FIFA Kwallon Kafa Ghana

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Ghana ya yi murabus

media
Shugaban hukumar kwallon kafa na Ghana Kwesi Nyantakyi. AFP Photo/Carl DE SOUZA

Shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Ghana Kwesi Nyantakyi ya ajiye mukaminsa sa’o’i bayan da hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, ta dakatar da shi daga shiga dukkanin harkokin wasanni a gida da kasashen ketare tsawon watanni 3.


A yau Juma’a ne dai hukumar FIFA, ta ce umarnin ya soma aiki ne nan take, bayan da kwamitinta na da’a ya samu shugaban hukumar kwallon kafar ta Ghana da laifi dumu-dumu wajne aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rasahawa.

FIFA ta samu Kwesi Nyantakyi da laifin neman dala miliyan 11 daga wasu manema labarai da suka yi badda kama a matsayin masu zuba hannun jari a fagen wasanni.

Zalika an samu shugaban hukumar kwallon ta Ghana da laifin yunkurin yin sama da fadi da kudi akalla dalamiliyan 5, daga cikin yarjejeniyar shekaru 5, da hukumar kwallon kafar kasar ta Ghana ta kulla da wani kamfani.