rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burundi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaba Pierre Nkurunziza ba zai tsaya takarar zaben shekarar 2020

media
Pierre Nkurunziza shugaban kasar Burundi REUTERS/Evrard Ngendakumana

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya sanar da cewar ba zai tsaya takarar shekarar 2020 ba, duk da rade radin cewar sauya kundin tsarin mulkin da ya kaddamar zai bashi damar tsayawa takara.


Shugaba Pierre Nkurunziza dake jawabi gaban magoya bayan sa da kuma jami’an diflomasiya, ya baiwa marada kunya wajen sanar musu da cewar ba zai yi amai ya tande ba, wajen sake takarar shugaban kasar, inda yake cewa wa’adin mulkin sa zai kare a shekarar 2020, kuma daga wannan babu sabuwar takara.

Sai dai yan adawa sun bayyana rashi gamsuwar su  tareda nuna shaku dangane da wadanan kalamai daga Shugaban kasar Pierre Nkurunziza.