rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Afrika ta kudu da kujerar memba a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya

media
Taron kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a New York REUTERS/Eduardo Munoz

A jiya juma’a ne aka zabi kasashen Jamus, Belgium, Afrika ta Kudu, Indonesia da jamhuriyar Dominicaine a matsayin memba ba na dindin ba a kwamity tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.


Wakilan kasashen za su soma aiki kama daga watan Janairu shekara 2019 zuwa 2021.

Jamus ta samu goyan bayan kasashe 184, Belgium 181, Afrika ta kudu 183, Indonesia 144 sai Jamhuriyar Dominicaine shine karo na farko da kasar ta shiga sahun wakilai a wannan kujera ta samu kuri’u 184.

Kwamity tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na da membobi 15, biyar daga cikin su na da matsayin memba dake da kujeru na dindin da suka hada da Amurka, Rasha, China, Faransa, Ingila.