rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wanke Jean Pierre Bemba daga tuhuma ya bar baya da kura

media
Magoya bayan Jean Pierre Bemba a Kinshasa JOHN WESSELS / AFP

Kwana daya bayan da kotun hukunta manyan Laifuka ta sanar da wanke tsohon madugun yan tawaye kuma tsohon mataimakin Shugaban Jamhuriyar Demukuraddiyar Congo Jean Pierre Bemba aka yankewa hukunci dauri na shekaru 18.


Magoya bayan sa na ci gaba da nuna farin cikin su ,duban magoya bayan tsohon madugu yan tawayen Jamhuriyar Demokurradiyar Congo sun kali zaman shara’ar ta talabijen ,yayinda kungiyoyin kare hakokin bil adam a kasar da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya suka nuna damuwa dangane da wannan sakamako, da suke dangatawa da rashin mutunta iyalan da suka rasa na su a kisan da magoyan bayan Bemba suka aikata a wacan lokaci.