rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun ICC ta sallami Jean Pierre Bemba

media
Jean-Pierre Bemba Tsohon mataimakin Shugaba Joseph Kabila REUTERS/JERRY LAMPEN

Kotun hukkunta masu manyan laifuka ta duniya ICC, ta sallami Jean Pierre Bemba a yau talata ,Jean Pierre Bemba wanda a can baya ta yankewa hukuncin daurin shekaru 18 bisa aikata laifukan yaki.


A shekarar 2016 kotun ta samu Bemba da laifin cin zarafin dan adam, baya ga sauran laifukan yaki, a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a shekarun 2002 da 2003, bisa zarginsa da gazawa wajen hana dakarunsa yi wa fararen hula kisan gilla da kuma aikata fyade.

Sai dai a lokacin da take sanar da soke hukuncin farkon, daya daga cikin alkalan kotun ta ICC, Christine Van den Wijingaert ta ce, alkalai a 2016, sun gaza la’akari da cewa Bemba ya yi iyaka kokarinsa wajen hana aikata laifukan yakin, bayan da aka sanar da shi abinda ke faruwa, dan haka bai kamata a kamashi da laifin da wasu dakarunsa suka aikata ba.

Kungiyar kare hakkin dan adam da Amnesty International ta bayyana sabon hukuncin a matsayin gagarumin koma baya, ga akalla fararen hula 5,000 da suka rayu, bayan cin zarafin da mayakan Jean Pierre Bemba sukai musu.