rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Zaben Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu dattawan Najeriya na bukatar Buhari ya kori Shugaban INEC da na yan Sanda

media
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu

Wasu dattawan da suka fito daga yankin kudu maso kudancin Najeriya da tsakiyar Kasar, sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kori Shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakub da sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris.


Wannan ya biyo bayan zargin kusancin shugaban hukumar zaben da shugaban kasa da kuma karya doka da odar da ake yi ma sufeto Janar Idris.

A watan Maris na shekara ta 2017 ne hukumar zaben Najeriya INEC, ta sanya ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2019 a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa da na 'Yan Majalisun Tarayya.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta nuna cewar za a gudanar da zaben Gwamnoni da na 'Yan Majalisun Jihohi a ranar 2 ga watan Maris.

INEC ta dai bai wa ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da zaben cikin tsari tare da daukan mataki kan duk wani jami’inta da aka samu da aikata laifin karya dokokin zabe.