Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro sun gano haramtaccen gidan sayen jini a Lagos

Rundunar ‘yansandan Najeriya ta cafke wani magidanci da ke gudanar da haramtaccen asusun tara jini a garin Lagos da ke kudancin kasar.Rahotanni sun ce mutumin ya dau tsawon lokaci ya na tafiyar da sana’ar sayen jinin daga jikin bil’adama, wanda kuma rundunar ta ce bashi da sahalewar hukuma ko kuma kwarewa a fannin.

Najeriyar wadda ke matsayin jagaba ta fuskar arzikin man fetur a Afrika, galibin al’ummarta miliyan 180 na rayuwa cikin talauci, dalilin da ke tilastawa wasu saba doka don samun kalaci.
Najeriyar wadda ke matsayin jagaba ta fuskar arzikin man fetur a Afrika, galibin al’ummarta miliyan 180 na rayuwa cikin talauci, dalilin da ke tilastawa wasu saba doka don samun kalaci. REUTERS/Austin Ekeinde
Talla

Rundunar ‘yansandan ta fara gudanar da bincike kan magidancin wanda aka bayyana sunanshi da Achegbulu Paul, wanda ta ce bashi da wata shaidar karatun bangaren lafiya haka zalika babu wata hukuma da ta sahale masa gudanar da bankin daukar jinin.

Kawo yanzu dai babu dai tabbacin inda Mr Paul ke kai jinin don sayarwa, ko da dai yayi ikirarin samun kwarewa a wata kwalejin horar gwaje-gwajen jini.

A makon da ya gabata ne dai Mr Paul ya zuki jinni har manyan roba biyu daga jikin wani kankanin yaro mai shekaru 17 tare da biyansa Naira dubu 4 daga bisani kuma bayan kwanaki 5 ya kara zukar roba biyu, matakin daya sa yaron faduwa ya soma inda aka garzaya da shi asibi.

Bayan isar jami’an tsaro ginin da Mr Paul ke gudanar da haramtacciyar harkallar asusun jinin, sun gano robobin jinni manya akalla bakwai wadanda bai kai ga siyarwa ba.

Najeriyar wadda ke matsayin jagaba ta fuskar arzikin man fetur a Afrika, galibin al’ummarta miliyan 180 na rayuwa cikin talauci, dalilin da ke tilastawa wasu saba doka don samun kalaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.