Isa ga babban shafi
ECOWAS-CEDEAO

Buhari ya ki amincewa da karbar shugabancin ECOWAS

Wata jarida da ake buga ta a Paris na kasar Faransa la Lettre du continent ta bayyana cewa duk da cewa shugaban Togo Faure Gnassingbe na Togo ya kammala wa’adin shugabancin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO akwai alamun shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kamata ya karbi ragamar shugabancin ya ki karba.

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Jaridar Faransan mai suna La Lettre Du Continent ta ruwaito cewa Shugaban Najeriya ya ki karbar ragamar shugabancin kungiyar a wata wasika daya aikewa Shugabannin kasashen yankin.

A cewar jaridar a tsakiyar wannan wata na yuni ne dai ya kamata Shugaban Togo Faure Gnassingbe ya mika mukamin ga shugaba Buhari, amma sai ya kasance Buhari yaki karban mukamin wanda hakan za ya bayar da dama domin gudanar da taron shugabannin kungiyar kasashen yankin cikin lokaci sai ga shi an dage taron har zuwa watan gobe.

Jaridar tace duk da cewa babu karin bayani dangane da dalilansa na kin karban shugabancin kungiyar, to amma wasu na ganin shugaba Buhari dake shirin tsayawa takara a zaben badi na kasar, na son mayar da hankulansa ne kan wannan yakin neman zabe dake gabansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.