rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da jirage Zamfara

media
Yanzu haka dai adadin 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a biranen Jihar ya tasamma dubu 10, yayinda rundunar ke cewa tana daukar matakan kawo karshen matsalar. Reuters

Rundunar sojin saman Najeriya ta aike da karin jirage biyu ga rundunarta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar zamfara karkashin shirin kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro a jihar Zamfara.Matakin rundunar na zuwa ne a dai dai lokacin da yawan ‘yan gudun hijira da suka kauracewa kauyukansu sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar ta Zamfara ke tasamma dubu 10.


Kwamandan rundunar 207 da ke yaki da ayyukan ta’addancin a Zamfara Kaftin Caleb Olayera ta hanyar aiki da jiragen Shalkwaftar ne za a iya kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

A cewar kwamandan maimakon jiran karin dakaru daga jihohin Kano da Bauchi yanzu jiragensu za su fara tashi daga birnin Gusau don kai dauki a sassan da ke cikin matsala ta hanyar shawagi a sararin samaniya.

Rundunar dai ta samu karin akalla jirage biyu daga shalkwatarta ta kasa don fatattakar ‘yan bindigar da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar ta Zamfara.

Yanzu haka dai dubban al’ummar jihar ta Zamfara mazauna kauyuka wadanda suka samu tsira da rayukansu daga hare-haren ‘yanbindigar na ci gaba da samun mafaka a biranen jihar.