rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsohon Gwamnan Filato zai share shekaru 14 a kurkuku

media
Tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye Reuters

Wata kotu a Abuja dake Najeriya ta samu tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye, wanda yanzu haka yake wakiltar Plateau ta tsakiya a Majalisar Dattawa da laifin cin hanci da rashawa, inda ta daure shi shekaru 14 a gidan yari.


Hukumar EFCC ta zargi Dariye da laifufuka 23 da suka hada da karkata sama da naira biliyan guda da milyan 161 lokacin da yake rike da mukamin gwamna.

Mai shari’a Adebukola Banjoko ta ce hukunci na shekaru 14 bashi da zabin biyan tara.

Ana ci gaba da bankado wasu daga cikin laifukan tsofin Gwamnonin Najeriya da suka gudanar da shugabanci ba bisa gaskiya ba.