rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Adadin mutanen da suka mutu ya harin Damboa ya tasamma 50

media
Wata Majiya daga garin na Maiduguri ta tabbatar da mutuwar mutane 43 yanzu haka yayinda wasu 12 kuma ke ci gaba da jinya a asibiti. REUTERS/Emmanuel Braun

Hukumomin tsaro a birnin Maiduguri da ke jihar Borno sun tabbatar da karuwar adadin mutanen da suka mutu a harin kunar bakin waken da kungiyar Boko Haram ta kai garin Danbuwa ranar asabar din da ta gabata.


Adadin mutanen da harin kunar bakin waken na Damboa ya hallaka yanzu haka a cewar hukumomin ya tasamma 50 ko da dai ganau na cewa adadin ya ninka hakan.

A ranar asabar ne dai kungiyar ta Boko Haram ta yi amfani da wata kankanuwar yarinya wadda ta daura wa bom a jiki ta shiga cikin al’ummar da ke gudanar da shagulgulan sallah.

Wata Majiya daga garin na Maiduguri ta tabbatar da mutuwar mutane 43 yanzu haka yayinda wasu 12 kuma ke ci gaba da jinya a asibiti.

Hare-haren dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke ci gaba da ikirarin fatattakar mayakan ta hanyar daruruwan dakarun soji da ta girke a jihar ta Borno.