Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Mohammed Khalid Usman kan yanayin saukar ruwan sama da iska a daminar bana.

Wallafawa ranar:

Bisa dukkan alamu daminar bana a wasu yankunan yammacin Africa za ta iya tfka barna mai yawan gaske.A kasar Ivory Coast, Hukumomin kasar sun sanar da cewa an sami ambaliyar ruwan sama a ranakun Littinin da Talata a birnin Abidjan wadda ta hallaka mutane 18.Zalika a Najeriya kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya sanar da cewa mutane 8 suka hallaka sakamakon ruwan sama da iska da ambaliyar da aka samu a jihar Bauchi.La’akari da yadda daminar bana ta kunno kai ne ya sa Garba Aliyu Zaria ya tuntubi, Farfesa Mohammed Khalid Usman na Jamiar Ahmadu Bello da ke Zaria wanda yayi tsokaci tare da jan hankali kan matakan da ya da ce a dauka domin rage kaifin hadarin da ka iya tasowa jama’a.

Wasu daga cikin mazauna kauyen Amassoma a jihar Bayelsa, ranar ga watan Oktoba, 2012, bayan da ambaliyar ruwa ta tilasta musu yin kaura.
Wasu daga cikin mazauna kauyen Amassoma a jihar Bayelsa, ranar ga watan Oktoba, 2012, bayan da ambaliyar ruwa ta tilasta musu yin kaura. REUTERS/Tife Owolabi
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.