rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamaru ta tabbatar da mutuwar Jami'an tsaro 81 a rikicin 'yan aware

media
Gwamnatin kasar ta ce ana bukatar sama da cfa milyan dubu 12 kimanin Euro milyan 20 domin gudanar da ayyukan jinkai a yankin STRINGER / AFP

Daga lokacin da fada ya barke tsakanin ‘yan aware da kuma dakarun gwamnatin Kamaru, akalla jami’an tsaron kasar 81 ne suka rasa rayukansu kamar dai yadda alkalumma ke nunawa.


Sojoji 74 da kuma ‘yan sanda 7 ne suka hallaka daga karshen shekarar bara zuwa yau a cewar wasu alkalumman ma’aikatar tsaro da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ta samu kofinsa.

Har ila yau alkalumman na nuni da cewa akwai fararen hula sama da dari daya da suka rasa rayukansu a wannan rikici da ke faruwa a yankin arewa maso yamma da kuma kudu maso gabashin kasar ta Kamaru.

Wasu daga cikin abubuwa na assha da suka fara sakamakon wannan rikici sun hada da kone makarantun boko 120 wadanda gwamnatin ta ce ‘yan aware ne suka kona su.

Gwamnatin kasar ta ce ana bukatar sama da cfa milyan dubu 12 kimanin Euro milyan 20 domin gudanar da ayyukan jinkai a yankin