Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun tasamma 100 - INEC

Hukumar zaben Najeriya ta ce ga alama adadin jam’iyyun siyasar da za su tsayar da ‘yan takara a matakai daban daban zai haure dari daya a zaben da za a gudanar cikin shekara mai zuwa a kasar.

Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Shugaban hukumar shirya zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu
Talla

Shugaban hukumar zaben Pr Mahmood Yakubu, wanda ke jawabi a gaban taron masu ruwa da tsaki a harkar zaben, ya ce kungiyoyin siyasa 138 ne suka gabatar da bukatar neman rajistar kasancewa jam’iyyun siyasa a gaban hukumarsa,

A game da wadanda za su kada kuri’a a zaben na badi kuwa, Pr Yakubu ya ce adadin zai kai mutane milyan 80.

A makon da ya gabata ne wasu dattawan da suka fito daga yankin kudu maso kudancin Najeriya da tsakiyar Kasar, su ka bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya kori Shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmud Yakub da sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris bisa zargin su da aikata ba dai-dai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.