rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Morocco Algeria

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Majalisar Dinkin Duniya ta aike da Manzo zuwa Algeria

media
Horst Kohler Manzo na MDD ya na ganawa da sakataren kungiyar Polisario Brahim Ghali RYAD KRAMDI / AFP

Manzo na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin yammacin Sahara Horst Koehler ya gana da ministan Algeriya na harakokin waje Abdel Kader Messahel a wata ziyara da ya kadamar zuwa yankin da nufi sake dawo da kasashen Morocco da kungiyar Polisario a teburin tattaunawa.


Jamiā€™in na Majalisar Dinkin Duniya zai yi amfani da wannan dama domin ziyartar wasu sansanonin yan gudun hijira na yan Sarraoui a Tindouf dake kudu maso yammacin yankin wanda ke a matsayin cibiya ga kungiyar ta Polisario.

Morocco ta kama yankin yammacin Sahara ne a shekara ta 1975 bayan ficewar turayan mulkin malaka na kasar Spain, wanda tun a lokacin ne kungiyar Polisario ta shiga yakin neman samun yancin kai.